Isa ga babban shafi

Kwararrun Amurka za su ziyarci Gambia bayan mutuwar tarin yara saboda cutar koda

Kasar Amurka zata tura tawagar masana harkar lafiyar ta zuwa Gambia domin gudanar da bincike akan dalilin mutuwar tarin kananan yara sakamkon lalacewar kodarsu da ake dangantawa da ambaliya ko kuma shan maganin zazzabin cizon sauro.

Wasu kanan yara a kauyen Bujinha, na kasar Gambia, a cikin watan Maris na shekarar 2022.
Wasu kanan yara a kauyen Bujinha, na kasar Gambia, a cikin watan Maris na shekarar 2022. AFP - MUHAMADOU BITTAYE
Talla

Ma’aikatar lafiyar Gambia ce ta sanar da samun karuwar yaran dake mutuwa sakamakon cutar koda wadanda ke tsakanin watanni 5 a duniya zuwa shekaru 4, inda aka bayyana mutuwar yara 28 cikin kankanin lokaci.

Tuni hukumomin kasar suka kaddamar da bincike inda suka bayyana wata cuta da kuma shan wani maganin farasetamol a matsayin abinda ke haifar da matsalar.

Ma’aikatar lafiyar kasar ta kuma zargi ambaliyar ruwan da aka samu a yan makwannin da suka gabata, wadda ta mamaye wasu sassan kasar.

Sanarwar ma’aikatar tace gwajin likita da akayi akan samfurin da aka dauka a jikin yara, ya nuna dalilin da ya sa aka samu karuwar mutuwarsu, abinda ya sa aka haramta amfani da maganin farasetamol a cikin kasar.

Hukumomin lafiyar kasar na hadin kai da jami’an Hukumar lafiya ta duniya domin shawo kann matsalar, yayin da Amurka tace a cikin kwanaki masu zuwa zata tura jami’anta domin gudanar da bincike akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.