Isa ga babban shafi

An cafke sojojin Congo 75 da ake zargi da cin amanar kasar

Hukumomin Jamhuriyar Demokuradiyar Congo sun cafke sojojin kasar 75 kan zargin su da yi wa kasar zagon kasa a yakin da take yi da ‘yan tawayen M23 a yankin gabashin kasar.

Wasu dakaun Jamhuriyar Dimokaridiyya Congo a yayin sintiri a garin Beni.
Wasu dakaun Jamhuriyar Dimokaridiyya Congo a yayin sintiri a garin Beni. MONUSCO/Abel Kavanagh
Talla

Wannan na zuwa ne mako guda da mahukuntan kasar suka sanar da kama tare da cafke babban kwamandan da ke jagorantar yaki da ‘yan tawayen na M23 bayan an zarge shi da hada baki da ‘yan tawayen don ci gaba da yi wa kasar barna.

A wata hira da sashen Faransa na RFI, shugaban Jamhuriyar Demokuradiyar Congo, Felix Tshisekedi ya tabbatar da kamen da suka yi wa babban kwamandan sojin , yana mai cewa, suna zargin sa da cin amanar kasa kuma za su ci gaba da gudanar daa  bincike a kansa.

Tun bayan kamen da aka yi wa Janar Philemon Yav Irung, al’ummar kasar suka fantsama kan tituna domin gudanar da zanga-zangar neman ganin an murkushe ‘yan tawayen kasar na M23, yayin da suka nuna bacin ransu kan batun alakar da ke tsakanin ‘yan tawayen da babban sojan.

An dai ce, Janar din ya jima cikin kyakkyawar alaka tsakaninsa da ‘yan tawayen da ke cin karansu babau babbaka a birnin Goma da ke arewacin Kivu, yayin da a baya-bayan nan, aka kara gano sojoji 75 da su ma aka ce suna yi kasar zagon kasa a wannan yakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.