Harin kunar bakin wake na Al-Shabaab ya kashe mutane 7 a Somalia
Rundunar sojojin Somalia da kuma shaidun gani da ido, sun ce wani harin kunar bakin wake da kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kai wa a Mogadishu babban birnin kasar, ya kashe akalla mutane bakwai tare da jikkata wasu a jiya Lahadi.
Wallafawa ranar:
Daya daga cikin kwamandojojin Sojan Somalia Abdul Adnan, ya ce wani dan ta’adda ne ya tarwatsa kansa da safiyar jiya Lahadi a kusa inda ake daukar sabbin kuratan sojoji a wani sansanin soja da ke kudancin birnin Mogadishu.
A farkon watan nan ne dai, mayakan Al Shebaab suka kashe fararen hula akalla 19, yayin wani hari da suka kai a yankin tsakiyar kasar.
A watan Agusta, kungiyar Al-Shabab din ta kaddamar da wani gagarumin hari a wani otel a birnin Mogadishu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 21 tare da jikkata 117.
Shugaban Somalia, Hassan Sheikh Mohamud yana fuskantar sake bayyanar kungiyar Al-Shabaab tun bayan da aka zabe shi a watan Mayu, kuma ya sha alwashin yin fito na fito da ita da zumar murkushe ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu