Isa ga babban shafi
Rikicin Somalia

Kimanin sojoji 30 sun mutu a harin da Al-Shabaab ta kaiwa sansanin AU

Jami'an soji da wasu shaidun gani da ido sun ce mayakan kungiyar Al-Shabaab dauke da muggan makamai sun afkawa wani sansanin sojojin kungiyar tarayyar Afrika AU da ke Somalia a ranar Talata, inda aka yi kazamar arrangamar da ta yi sanadin salwantar rayuka a bangarorin biyu.

Sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar hadin kan kasashen Afirka AU a kasar Somalia.
Sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar hadin kan kasashen Afirka AU a kasar Somalia. © Getty Images
Talla

Bayanai sun ce, rundunar sojojin na AU ta aike da jirage masu saukar ungulu bayan farmakin da mayakan na Al Shebaab suka kaddamar kan sansanin sojojin wanzar da zaman lafiya da dauke da dakarun Burundi, wanda ke kusa da Ceel Baraf, wani kauye mai tazarar kilomita 160 daga arewa maso gabashin Mogadishu babban birnin Somalia.

Wani babban hafsan sojin Burundi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kimanin sojoji 30 ne suka mutu, wasu 22 kuma suka jikkata, yayin da wasu goma suka bace, said ai babu wani tabbaci game da adadin mutanen da aka kashe daga jami'an Somalia ko AU.

Dakarun wanzar da zaman. lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka AU a birnin Mogadishu da ke kasar Somalia.
Dakarun wanzar da zaman. lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka AU a birnin Mogadishu da ke kasar Somalia. © REUTERS/Feisal Omar

Kwamandan sojojin yankin Mohamed Ali ya shaida wa AFP ta wayar tarho cewa mayakan na Al Shebaab sun kaddamar da harin ne ta hanyar amfani da wata mota makare da bama-bamai, kafin daga bisani a fara musayar wuta tsakaninsu da dakarun na kungiyar AU.

Wannan dai shi ne hari na farko da aka kai kan sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na AU, tun bayan da aka sabunta rundunar wanzar da zaman lafiya ta AU a Somalia gami da sauya mata suna daga AMISOM zuwa ATMIS a ranar 1 ga watan Afrilu.

Majiyar sojan Burundi ta ce mayakan Al Shebaab kimanin 400 ne suka afkawa sansanin sojin na AU bayan da suka tarwatsa wasu bama-bamai da motoci guda biyu. Daga nan ne sojojin Burundin suka koma wani tsauni da ke kusa inda suka ci gaba da fafatawa, tare da samun tallafin jirage marasa matuka da jirage masu saukar ungulu.

A wata sanarwa da mayakan masu ikirarin Jihadi suka fitar, sun ce sun karbe iko da sansanin bayan kashe sojojin kungiyar Tarayyar Afirka 173, tare da fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna gawarwakin sojojin da aka kashe a kwance a kasa.

Ba a dai iya tantance adadin mutanen da suka mutu da bidiyon ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.