Isa ga babban shafi
Somalia

Dan kunar bakin wake ya kashe mutane 13 a Somalia

Akalla mutane 13 suka mutu a garin Beledweyne da ke tsakiyar kasar Somaliya a ranar Asabar, bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a wani gidan cin abinci da shaidu suka ce cike yake da jami'an gwamnatin yankin da sauran 'yan siyasa.

Wani yanki a birnin Mogadishu da aka kai harin kunar bakin wake.
Wani yanki a birnin Mogadishu da aka kai harin kunar bakin wake. © REUTERSs/Feisal Omar
Talla

Tuni kungiyar al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin, day a jikkata wasu mutane 18, baya ga rayukan day a lakume.

Cikin makwanni biyun da suka gabata, sai da kungiyar ta Al Shebaab ta kai wasu hare-haren kashi biyu a sassan kasar Somalia.

Jami’an ‘yan sanda da na gwamnati sun tabbatar da harin kunar bakin waken da aka kai gidan cin abincin, amma ba su bayyana adadin wadanda suka mutu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.