Isa ga babban shafi

WHO ta fara binciken kan maganin Indiya da ya kashe yara 66 a Gambia

Hukumar lafiya ta duniya ta fitar da sanarwar game da wasu magungunan tari guda hudu da Kamfanin Maiden Pharmaceuticals ya yi a Indiya, inda ta yi gargadin cewa za a iya danganta magungunan da mutuwar yara 66 a Gambia.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus kenan
Shugaban hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus kenan REUTERS - DENIS BALIBOUSE
Talla

Hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta kuma yi gargadin cewa, mai yiwuwa an rarraba gurbatattun magungunan a wajen kasar da ke yammacin Afirka, inda ake fargabar hakan ka iya yaduwa a duniya.

Shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida wa manema labarai cewa akwai yuwuwar cewa maganin sanyi da tari guda hudu da ake magana a kai na da alaka da ciwon koda da kuma mutuwar yara 66.

Tedros ya ce hukumar ta WHO tana kuma ci gaba da gudanar da bincike kan kamfanin tare da hukumomin da abun ya shafa a Indiya.

Dangane da faɗakarwar samfuran magungunan da WHO ta bayar guda hudu sune, Promethazine Oral Solution, Kofexmalin Baby Cough Syrup, Makoff Baby Cough Syrup da Magrip N Cold Syrup.

Har ya zuwa yau, masana'antar da aka bayyana ba ta ba da cikakken bayani ga WHO kan aminci da ingancin wadannan magungunanba.

Bincike daga dakin gwaje-gwaje na samfuran magungunan ya tabbatar da cewa sun kunshi gurbatattun sinadarin diethylene glycol da ethylene glycol da ya wuce kima.

Ma'aikatar lafiya ta Gambia ta bukaci asibitoci a watan da ya gabata da su daina amfani da maganin paracetamol na yara, har sai an kammala bincike, bayan da akalla yara 28 suka mutu sakamakon ciwon koda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.