Isa ga babban shafi

Gambia: 'Yan sanda na binciken mace-macen da ke da nasaba da wani maganin tari

'Yan sanda a Gambia sun fara bincike kan mutuwar yara 66, wadanda ake alakanta su da wasu nau'ikan maganin tari guda hudu da aka shigo da su daga kasashen waje.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce tuni ta fara bincike a kai tare da hukumomin Indiya, wato inda kamfanin ya ke
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce tuni ta fara bincike a kai tare da hukumomin Indiya, wato inda kamfanin ya ke AFP - MILAN BERCKMANS
Talla

Fadar shugabancin kasar, ta bukaci hukumomin da ke kula da magunguna da na masu shigo da kayayyaki da su gudanar da bincike a kan su.

Al’ummar Gambia dai sun shiga damuwa ainun kana bin da ya faru, inda suka diga ayar tambaya kan hukumomin da ke sanya idanu kan kayayyakin da ake shigarwa kasar.

A ranar Laraba ne, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ba da sanarwa game da maganin tari guda hudu, tana mai gargadin cewa za a iya danganta su da sinadaran da ke taba koda da kuma mutuwar yara a watan Yuli, Agusta da Satumba.

Jami’an kiwon lafiya na Gambia da ma’aikatan kungiyar agaji ta Red Cross yanzu haka suna bi gida-gida, da kuma shagunan sayar da magunguna da kasuwanni, domin binciko maganin da sauran magunguna.

Sama da kayayyaki 16,000 ne aka gano ya zuwa yanzu kuma tuni hukumomi suka killace su.

A ranar Juma'a, shugaba Adama Barrow ya yi jawabi ga al'ummar kasar, inda ya bayyana alhininsa game da asarar rayuka da aka yi, yana mai cewa za a binciki tushen gurbatattun magungunan.

Shugaban ya sanar da shirin bude dakin gwaje-gwajen da zai rika tabbatar da ingancin magunguna da kuma nazarin dokoki da ka'idojin da suka dace na magungunan da ake shigowa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.