Isa ga babban shafi

Uganda ta haramtawa masu magungunan gargajiya bayar da maganin Ebola

Shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya bada umarnin haramtawa masu maganin gargajiya bada maganin cutar Ebola, a kokarin da ake yi wajen dakile yaduwar cutar wadda zuwa yanzu ta hallaka mutane 19 a sassan kasar da ke gabashin Afrika.

Shugaban Uganda Yoweri Museveni.
Shugaban Uganda Yoweri Museveni. REUTERS - ABUBAKER LUBOWA
Talla

A wani jawabin kai tsaye da shugaban ya gabatar ta gidan talabijin, Museveni ya kuma umarci jami’an tsaro su kama duk wani da ake zargi ya na fama da zazzabi mai zafi kuma ya ki mika kansa cibiyar killace masu fama da cutar.

Umarnin dai ya biyo bayan wani taron ministocin Uganda da ya gudana a Kampala, don tattauna matakan gaggawa game da cutar da ta kashe mutum na farko cikin kasar a watan jiya, karo na farko da ake ganin barkewar cutar tun bayan shekarar 2019.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaidawa taron cewa, nan da makwanni masu zuwa za'a fara gwajin magungunan da za'a yi amfani da su wajen yaki da nau'in cutar da aka samun yaduwar ta a kasar Uganda wacce a halin yanzu babu wani rigakafin ta.

Sanarwar da hukumar ta WHO ta fitar ta ce, akwai mutane 54 da aka tabbatar sun kamu da cutar, yayin da 19 suka mutu tun bayan da aka fara samun bullar ta a gundumar Mubende da ke tsakiyar kasar a ranar 20 ga watan Satumban da ya gabata.

Shugaba Museveni ya ce wani dan asalin Congo mai shekaru 45 ne kadai ya mutu sanadiyar cutar a babban birnin kasar Kampala, bayan da ya tsere dada cibiyar killace masu dauke da cutar a Mubende a lokacin da wani dan uwan sa ya mutu sanadiyar cutar.

A cewar shugaban kawo yanzu an killace mutanen da sukayi mu’amulla da shi a kokarin dakile yaduwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.