Isa ga babban shafi

Uganda da Habasha sun goyi bayan cirewa Somalia takunkuman hana sayen makamai

Gwamnatin Somalia na samun goyon baya kan fafutukar da ta ke na ganin an janye takunkumin da aka kakaba mata na hana shigar da makamai kasar, inda a baya bayan nan, Habasha ta bi sahun Uganda wajen goyon bayan janye matakin.

Sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar hadin kan kasashen Afirka AU da ke taimakawa Somalia yaki da kungiyar Al Shebaab.
Sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar hadin kan kasashen Afirka AU da ke taimakawa Somalia yaki da kungiyar Al Shebaab. © Getty Images
Talla

A cikin watan Nuwamba ake sa ran kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'a kan sabunta takunkumin haramta saidawa Somalia makamai, wanda gwamnati ta ce, cire shi zai taimaka mata wajen yakar mayakan ‘yan ta’adda na Al Shebaab.

Goyon bayan da Habasha ta bai wa Somalia, ya zo ne bayan da a watan Yuli, gungun mayakan Al Shebaab suka kutsa cikin iyakarta, a lokacin da su ke gujewa hare-haren sojojin Somalia.

A halin yanzu, shekaru akalla 30 kenan aka shafe takunkuman hana shigar da makaman na aiki kan Somalia, wadanda shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud da Firaministan Habasha Abiy Ahmed suka ce lokaci ya yi da za a janye su, domin ba da damar kaddamar da cikakken yaki kan mayakan Al Shebaab.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.