Isa ga babban shafi

Harin Al-Shebaab ya kashe mutane 12 a Somalia ciki har da manyan jami'am gamnati

Akalla mutane 12 ne suka mutu ciki har da wasu manyan jami’an gwamnatin Somalia a tagwayen hare-haren bom da kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kai wa a birnin Beledweyne na tsakiyar kasar.

Wani yanki da Al Shebaab ta farmaka a Somalia.
Wani yanki da Al Shebaab ta farmaka a Somalia. AFP - HASSAN ALI ELMI
Talla

Kwamandan ‘yan sandan yankin Mohamed Moalim Ali da ke tabbatar da faruwar harin, ya bayyana cewa Al-Shebaab ta ajje wasu motoci biyu da ke makare da bama-bamai a gab da ofisoshin hukumomin yankin birnin na Beledweyne.

Dakarun Somalia da kawayen su na kasashen waje na ci gaba da kai wa mayakan kungiyar hari a 'yan makwannin nan, inda ko a ranar litinin din makon nan sai da gwamnatin kasar ta sanar da kashe Abdullahi Yare, babban jigo a kungiyar ta Al-Shabaab, a wani harin jiragen yakin hadin gwiwar ranar Asabar din da ta gabata a kudancin kasar.

Sabon shugaban kasar ta Somalia Hassan Sheikh Mohamud, ya sha alwashin yaki da masu ikirarin jihadi, bayan wasu munanan hare-hare da suka kai, ciki har da na wani otel da suka kwace ikon sa har na sa'o'i 30 a Mogadishu babban birnin kasar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21.

A watan da ya gabata Mohamud ya bukaci 'yan kasar da su kauracewa ziyartar yankunan da kungiyar Al-Shabaab ke iko da su, yayinda dakarun gwamnati da ke samun goyon bayan mayakan sa-kai suka kaddamar da hare-hare a yankin Hiraan, wanda fadar mulkinsa ke birnin Beledweyne.

Jami’an soji sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa mazauna yankin sun yanke shawarar daukar makamai domin yakar ‘yan ta’addan, wadanda ake zargi da karbar kudade daga hannunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.