Somalia ta rufe shafukan Intanet masu alaka da Al Shebaab
Gwamnatin Somalia ta sanar da rufe wasu shafukan yanar gizo da ta ce suna taimakawa wajen yada farfagandar kungiyar al-Shabab da ke ikirarin kishin Islama.
Wallafawa ranar:
Sanarwar ta kuma gargadi mutane kan yada duk wani abu da ka iya karfafawa mayakan na Al Shebaab gwiwa wajen kai hare-hare da sunan jihadi.
A makwannin baya bayan nan dai, sojojin Somalia sun sami jerin nasarori yayin fafatawar da suka yi da mayakan Al Shebaab, sai dai kungiyar na ci gaba da kai hare-haren bama-bamai da na kunar bakin wake.
Jim kadan bayan hawansa kan mulkin Somalia a watan Yuni, shugaba Hassan Sheikh Mohamud, ya yi alkawarin murkushe kungiyar Al Shebaab.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu