Isa ga babban shafi

Somalia ta nada tsohon kwamandan Al-Shabaab a matsayin Ministan addini

Firaministan Somalia Hamza Abdi Barre ya bayyana nadin tsohon mataimakin shugaban kungiyar Al-Shabaab kuma kakakin ta a matsayin ministan harkokin addini na kasar.

Shugaba Hassan Cheikh Mohamoud.
Shugaba Hassan Cheikh Mohamoud. © AP - Farah Abdi Warsameh
Talla

Nadin nasa ya zo ne makwanni bayan da sabon shugaban kasar Hassan Sheikh Muhamud ya bayyana cewar, gwamnatinsa a shirye ta ke ta hau kan teburin tattaunawa da Al-Shabaab idan lokaci ya yi.

Al-Shabaab dai na yaki ne da gwamnatin kasar a cikin shekaru 15 da suka gabata, duk kuwa da dakarun kungiyar tarayyar Afrika da ke kasar don dakatar da ita.

Bayan nadin Barre da aka yi a ranar 25 ga watan Yunin da ya gabata, an tsammaci ya bayyana majalisar ministocinsa cikin kwanaki 30, amma aka fuskanci tsaiko saboda zaben kasar da ya samar da Mohamud a matsayin shugaba.

Nade-naden na jiya talata ya kuma kunshi mataimakin Firaminista da ministoci 25 da kananan ministoci 24 da mataimakan su a tawagar mai mambobi 75.

A watan Yuli, Shugaba Mohamud ya ce kawo karshen ta’addanci na bukatar wasu dabaru fiye da na Soji.

Sabuwar gwamnatin Somalia dai za ta fuskanci matsalar karancin abinci, ganin alkaluman da majalisar dinkin duniya ta fitar ya nuna cewar, kusan rabin mutanen kasar miliyan 7 da dubu dari ne ke fuskantar barazanar yunwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.