Isa ga babban shafi

Shugaban Somalia ya nada sabon Firaminista

Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud Roble ya nada dan majalisa Hamza Abdi Barre a matsayin sabon Firaministan kasar a jiya Laraba, nadin da yazo a daidai lokacin da kasar ta Somalia ke fuskantar kalubale da dama, da suka hada da iftila’in yunwa da kuma hare-haren mayakan kungiyar Al Shebaab.

Sabon Firaministan kasar Somalia Hamza Abdi Barre.
Sabon Firaministan kasar Somalia Hamza Abdi Barre. via REUTERS - PRESIDENTIAL PRESS SERVICE
Talla

Dan majalisar mai shekaru 48 daga jihar Jubaland mai kwaryakwaryar cin gashin kanta, ya maye gurbin Mohamed Hussein Roble, wanda a tsawon watanni 22 da ya shafe kan karagar mulki yayi fama da rikici tsakaninsa da tsohon shugaban kasa Mohamed Abdullahi Mohamed da aka fi sani da Farmajo, takaddamar da tayi ya yi barazanar sake jefa Somalia cikin wani nau’in na tashin hankali.

Hassan Mahamoud wanda ya taba zama shugaban kasa tsakanin shekarar 2012 zuwa 2017 -- ya bayyana zabinsa na sabon Firaminista ne kwanaki shida kacal bayan rantsar da shi a bikin da ya gudana a birnin Mogadishu wanda ya samu halartar shugabannin kasashe da dama.

Kafin nasarar lashe zaben da Mahmoud yayi a tsakiyar watan Mayu, sai da aka shafe akalla shekara guda ana rikici tsakanin tsohon shugaba Farmajo da Firaministansa, abinda ake fatan ba zai sake maimaituwa a karkashin sabon jagorancin da aka samu ba.

Farmajo ne ya zabi Roble a matsayin Firaministan Somalia a watan Satumban shekarar 2020 amma sabani mai karfi ya rusa kyakkyawar alakar dake tsakanin jagororin biyu akan zaben shugabancin kasar da aka dade ana jinkirtawa da kuma tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.