An sanya dokar takaita zirga-zirga a Somalia gabanin zabe
A yau Asabar ‘yan sanda a Somalia suka sanar da ayyana dokar takaita zirga zirga a babban birnin kasar Mogadishu, tana mai bayyana fargabar tabarbarewar tsaro bayan da ta haramta duk wasu sabogogi na al’umma har zuwa kammala kada kuri’a a zaben shugaban kasar a gobe Lahadi.
Wallafawa ranar:
Gwamman ‘yan takara ne ke fafatwa a wannan zabe a kasar da ke fama da matsalar ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi, a yayin da take fama da barazanar yunwa.
Kakakin ‘yan sandan kasar Abdifatah Adan ya bayyana a wani taron manema labarai cewa daga yau Asabar da karfi 9 dacrabi na dare za a takaita zirga zirgar ababen hawa da mutane.
Tuni kawayen Somalia na kasa da kasa suka shaida wa hukumomin kasar cewa jinkirta zaben da aka yi sakamakon dambarwar siyasa yana da hadari ganin yadda ya dauke hankali daga yaki da kungiyar ‘yan ta’adda ta Al-Shabaab, mai ikirarin jihadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu