Isa ga babban shafi
Somalia-Farmanjo

Takaddama ta kaure tsakanin jagororin Somalia kan korar jakadan AU

Gwamnatin Somalia ta sallami wakilin kungiyar tarayyar Afrika da ke Mogadishu bayan zarginsa da yi mata katsalandan a harkokin cikin gida, ko da ya ke shugaba Mohammad Farmanjo ya yi watsi da umarnin, dai dai lokacin da rikici ke ci gaba da tsananta tsakanin jagororin biyu.

Shugaban Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed Farmajo, da Firaminista Mohamed Hussein Roble.
Shugaban Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed Farmajo, da Firaminista Mohamed Hussein Roble. © Caasimada Online
Talla

Firaminista Muhammad Hussein Roble da ke sanar da wannan mataki ya ce tuni aka bai wa Ambasada Francisco Medeira wa’adin sa’o’i 42 ya bar kasar, saboda zargin na shiga lamurran da bai shafe shi ba.

A jawabinsa kan matakin sallamar jakadan na Afrika, Firaminista Muhammad bai yi cikakken bayani kan laifin da wakilin ya yi ba, sai dai ya ce ya yi wa kasar kafar Angulu.

Har yanzu dai Mediera dan asalin kasar Mozambique bai mayar da martani kan sallamar sa daga Somalia ba, to amma kungiyar AU a hukumance ta ce za ta bayyana matsayar ta a nan gaba.

To sai dai masana na ganin sallamar ta sa za ta sake zafafa alakar siyasa da ke tsakanin Firaminista Roble da kuma shugaba Mohammad Abdullahi Mohammad da aka fi sani da Farmanjo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.