Isa ga babban shafi

Sabon rikici ya kunno kai tsakanin shugabannin Somalia

Fira Ministan Somalia ya kori wakilin kungiyar Tarayyar Afirka saboda aikata wasu ayyukan da suka yi hannun riga da matsayinsa, sai dai shugaban kasar ya ki amincewa da umarnin korar, lamarin dake nuna wata sabuwar baraka tsakanin shugabannin Somaliyan.

Shugaban kasar Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo.
Shugaban kasar Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo. Reuters/Feisal Omar
Talla

Ofishin Fira Minista Mohamed Hussein Roble ya ce dole ne wakilin Tarayyar Afirka, Francisco Madeira, ya fice cikin sa'o'i 48, ba tare da bayar da cikakken bayan ikan laifin da Madeira ya aikata da ya kai ga kora ba.

Fira Ministan kasar Somalia Mohamed Hussein Roble.
Fira Ministan kasar Somalia Mohamed Hussein Roble. AFP - STRINGER

Har zuwa lokacin wannan wallafa dai, Madeira, wanda ya fito daga Mozambique, bai ce komai kan batun ba, sai dai wani jami’in ofishin kungiyar Tarayyar Afirka dake Mogadishu ya ce za su mayar da martani ta hanyar wasika daga baya.

A watan Disamba, shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Mohammed da aka fi cewa Farmajo ya yi kokarin dakatar da ikon Fira Minista Mohammed Hussein Roble bisa zargin cin hanci da rashawa.

An dai shafe tsawon lokaci ana rikici tsakanin shugabannin biyu, abinda ya janyo jinkirtar da zaben 'yan majalisar dokoki, wanda aka fara a watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.