Isa ga babban shafi

'Yan majalisar Somalia sun kada kuri'ar zaben sabon shugaban kasa

'Yan majalisar dokokin Somalia suka kada kuri'a a zaben shugaban kasar da aka dade ana jira, inda 'yan takara da dama ke neman darewa kujerar shugabancin kasar da ke fama da rikici a yankin kahon Afirka, a daidai lokacin da take fuskantar hare-haren kungiyar Al Shebaab da kuma iftila’in fari.

Wani dan majalisar dokokin Somalia yayin kada kuri'a a zaben shugaban majalisar dokokin kasar, a filin jirgin saman Aden Adde dake Mogadishu, Somalia, 28 ga Afrilu, 2022.
Wani dan majalisar dokokin Somalia yayin kada kuri'a a zaben shugaban majalisar dokokin kasar, a filin jirgin saman Aden Adde dake Mogadishu, Somalia, 28 ga Afrilu, 2022. © REUTERS/Feisal Omar/File Photo
Talla

'Yan majalisar sun kada kuri'un nasu ne a karkashin tsauraran matakan tsaro a wani tanti da ke cikin harabar filin jirgin sama na Mogadishu, ba tare da wani motsi ba a babban birnin kasar, inda 'yan sanda suka kafa dokar hana fita har zuwa ranar Litinin.

An kuma soke tashin jirage, kamar yadda wani jami'i ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Gabanin gudanarsa dai, zaben ya sha suka daga bangarori masu hamayya da juna da ke zargin ba za a yi adalci ba, baya ga tsaikon da ya fuskanta da tsawon shekara guda, abinda ya sanya manyan kasashen duniya gargadin cewa jinkirin da aka samu sakamakon rigingimun siyasar kasar ta Somalia, hatsari ne babba da ka iya gurgunta yakin da ake yi da mayakan kungiyar Al Shebaab.

Ana sa ran zaben na yau Lahadi ya kawo karshen rikicin siyasar da ya barke a Somalia tsawon fiye da shekara guda, bayan karewar wa’adin mulkin shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed Farmajo a watan Fabrairun 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.