Isa ga babban shafi
Somalia-Siyasa

An zabi Hassan Sheikh Mohamud a matsayin shugaban Somalia

A Somalia, an zabi Hassan Sheikh Mohamud a matsayin shugaban kasa, biyo bayan zaben da aka gudanar a ranar Lahadi a kasar da ke fama da matsalar ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi, da kuma barazanar  matsanancin yunwa.

Hassan Cheikh Mohamoud shine sabon shugaban Somalia.
Hassan Cheikh Mohamoud shine sabon shugaban Somalia. © REUTERS/Feisal Omar
Talla

Bayan lokaci mai tsawo da aka kwashe ana kada kuri’a a fafatawa da aka yi da ‘yan takara 36, wanda aka watsa kai tsaye a  tashar talabijin ta kasar, a farfajiyar  majalisar dokokin kasar, tsohon shugaba Hassan sheikh Mohamud yaa samu kuri’u 214, sama da adadin da ya ke bukata ya doke shugaba mai ci, Mohammmed Abdullahi Mohammed, wanda ake wa inkiya da Farmajo.

An yi ta harba bindiga sama a babban birnin kasar, Mogadishu, lamarin da ke alamta murnar wannan nasara, inda da dama ke fatan cewa zaben zai kawo karshen rikita rikitar da aka shafe shekara guda ana yi, bayan da wa’adin mulkin Farmajo ya kare a watan Fabrairun 2021 ba tare da an gudanar da zabe ba.

Zababben shugaban Mohamud, wanda ya taba jagorantar kasar daga shekarar 2012 zuwa 2017, ya sha ranstuwar kama aiki jim kadan bayan da aka kammala kirga kuri’un da aka kada, inda daga nan ya gabatar da jawabi ga al’ummar kasar.

Yau tsawon shekaru 50 kenan rabon da a gudanar da zaben kada kuri’a kai tsaye a Somali, a maimakon haka, wani tsari mai sarkakiya ake bi, inda ‘yan mjalisar dokokin jihohi da wakilan kabilu ke zaben ‘yan majaisar dokoki na kasa, wadanda za su zabi shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.