Majalisar dokokin Somalia ta amince da nadin sabon Firaminista
Majalisar dokokin Somalia ta amince da nadin Hamza Abdi Barre a matsayin sabon Firaministan kasar, matakin da ya share fagen kafa sabuwar gwamnati a kasar dake yankin kuryar gabashin Afirka.
Wallafawa ranar:
Dukkanin ‘yan majalisa 220 da suka halarci zaman da aka yi a jiya Asabar ne suka tabbatar da nadin Firaminista Barre, inda kuma yayi rantsuwar kama aiki.
Sabuwar gwamnatin Somalia na fuskantar kalubale ta fuskokin tattalin arziki da tsaro, da suka hada da, bala’in yunwa da kuma barazanar kungiyar Al Shebaab dake hankoron kifar da gwamnati.
A baya bayan nan wani rahoton majalisar dinkin duniya ya bayyana cewar, kimanin 'yan Somalia miliyan 7 da dubu 100, kusan rabin al'ummar kasar, na fama da yunwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu