Isa ga babban shafi

Masu shigar da kara na son kotu ta yiwa Kunti Kamara hukuncin daurin rai da rai

Masu gabatar da kara a shari’ar farko da Faransa ta fara kan wani mai hannu a mummunan yakin basasar Liberia, sun nemi a yankewa tsohon kwamandan ‘yan tawayen da ake zargi da laifukan cin zarafin bil adama hukuncin daurin rai-da-rai.

Zaman sauraron shari'ar Kunti Kamara a birnin Paris na Faransa.
Zaman sauraron shari'ar Kunti Kamara a birnin Paris na Faransa. © Francois Mori / AP
Talla

Ana zargin Kunti Kamara mai shekaru 47 a kan laifukan da ya aikata a shekarar 1993 da 1994, wato shekarun farko rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 250 a tsakanin shekarun 1989 zuwa 2003.

Yayain yakin dai ai aikata manyan laifukan da suka kunshi kashe-kashen gilla da fyade, tare da guntule hannuwa da kafafun fararen hula a rikicin, kuma akasari yara kanana da jagororin ‘yan tawaye suka tilastawa shiga aikin soja ne suka aiwatar da wannan ta’asa a kan wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Kamara ne kwamandan yanki na kungiyar ‘yan tawayen Movement of Liberia for Democracy, kungiyar da ke yaki da National Patriotic Front ta tsohoin shugaban kasar Charles Taylor.

Ana zarginsa da azabtarwa, hadin baki wajen aikata laifukan cin zarafin bil adama, yi wa fararen hula kisan gilla, tare da taimakawa wajen yi wa ‘ya'ya mata fyade da kuma cin naman mutane.

Lauyar masu gabatar da kara Aurelie Belliot ta shaidawa kotu a Paris cewa laifukan Kamara sun salwantar da tarin rayuka a kasar ta Liberia yayin yakin basasar.

Sai dai Kamara ya musanta aikata laifukan da aka karanto mai a zarge zargen da ake masa a gaban kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.