Isa ga babban shafi

Dakarun Mali da Sojin hayar Wagner sun kashe fararen hula 13- Rahoto

Wasu majiyoyi sun ce dakarun Mali tare da wasu sojoji fararen fata da ake kyautata zaton mayakan kamfanin Wagner na kasar Rasha ne, sun kashe fararen hula 13 a wani kauye da ke yankin tsakiya a  kasar.

Wasu sojojin hayar Wagner.
Wasu sojojin hayar Wagner. AP
Talla

Wani dan siyasa a kauyen Guelledje da ke tsakiyar kasar Mali, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa da yammacin Lahadi ne wadannan sojoji tare da wasu fararen fata suka sauka kauyen.

Wani dan majalisar dokoki wanda shi ma ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce sun ji karar harbe harbe, kuma daga cikin wadanda aka kashe har da wasu mutane 3 daga iyali guda.

Wata majiya daga garin Guelledje ta ce an kai wa kauyen farmaki ne saboda yadda sojin Mali da na Wagner ke daukarsa a matsayin tungan ‘yan ta’adda.

Kasashen Faransa, Amurka da kawayenta na yammaci Turai,  sun zargi gwamnatin Mulkin sojin Mali da daukar dakarun hayar Wagner na kasar Rasha don yaki da ‘yan ta’addan da suka dade suna addabar kasar.

Sai dai gwamnatin sojin Mali ta musanta wannan zargi, tana main cewa sojoji fararen fata da ake gani tare da dakarunta suna aiki ne a matsayin masu bada horo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.