Isa ga babban shafi

Amurka ta zargi Sojin hayar Wagner da dagula lamurran tsaro a Mali

Gwamnatin Amurka ta zargi sojojin hayar kasar Rasha na kamfanin Wagner, da dagula lamurran tsaro a Mali, matsalar da wani babban jami’in kasar ke cewa ta wanzu ne sakamakon kura-kuran da sojojin kasar ta Mali da suka yi juyin mulki ke tafkawa, wajen aiwatar da manufofin tunkarar yaki da ta’addanci.

Wasu sojojin hayar Wagner.
Wasu sojojin hayar Wagner. AP
Talla

Tun bayan kwace mulkin da ta yi a shekarar 2020, gwamnatin sojin Mali ta juyawa Faransa baya, inda ta karkata ga Rasha a yakin da ta ke yi da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi.

Amurka, Faransa da sauran kasashen yammacin duniya sun dade suna zargin gwamnatin mulkin sojan Mali da daukar Wagner aiki, sai dai mahukuntan sun musanta hakan, inda suka ce suna aiki ne kai tsaye tare da gwamnatin kasar ta Rasha, ba wai kamfanin sojojin hayar ba.

Yayin ganawa da manema labarai, karamar sakatariyar harkokin siyasa a ma'aikatar harkokin wajen Amurka Victoria Nuland ta ce a halin yanzu Amurka ba ta iya bai wa Mali taimako ta fannin tsaro, tun bayan da sojojin kasar suka kulla alaka da sojojin haya daga Rasha na kamfanin Wagner.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.