Isa ga babban shafi

Kasashen Afirka na jaddada kadarorinsu a taron COP 27 na Masar

Shugaban kasar Kenya William Ruto ya yi kira a yau litinin a taron COP27 don amincewa da "bukatu na musamman na Afirka" a yakin da ake yi da dumamar yanayi.

Taron COP 27 a Masar
Taron COP 27 a Masar AP - Nariman El-Mofty
Talla

William Ruto a madadin kungiyar Afirka ya ce, "Asara da barna ba batun tattaunawar da ba za a iya cimmawa ba ne, kwarewa ce ta yau da kullum da kuma mafarkin rayuwa da miliyoyin 'yan Afirka ke fama da su.

A cewar Shugaba Ruto da ke Magana a madadin kungiyar Afirka, dangane da rashin son kasashe masu arziki na samar da wata manufa ta hadin gwiwa.

Saboda haka ya dace kuma wannan taron ya dauki matakan da suka dace don gane yanayi na musamman da bukatun Afirka.

A cikin shekaru 50 da suka gabata, fari ya kashe mutane rabin miliyan tare da yin asarar tattalin arzikin sama da dala biliyan 70 a yankin a cewar shugaban kasaer ta Kenya.

shugaba Ruto ya kara da cewa, "kahon Afirka, ciki har da Kenya, na fuskantar fari mafi muni cikin shekaru 40 da suka gabata.

Shugaban kasar Zambiya Hakainde Hichilema ya kara da cewa "Yayin da wannan COP27 ke faruwa a nahiyar Afirka da ke fama da matsalar sauyin yanayi ta hanyar ba da gudunmowa kadan a gare ta, muna sa ran wannan COP din zai magance muhimman matsalolinmu."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.