Isa ga babban shafi

Boko Haram ta kashe sojojin Chadi 10

Mayaka masu ikirarin jihadi sun kashe akalla sojojin Chadi 10 a wani hari da suka kaddamar musu a wata tungarsu da ke yankin kudancin kasar kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar.

Sojojin Chadi yayin atasaye a yankin Diffa dake Jamhuriyar Nijar.
Sojojin Chadi yayin atasaye a yankin Diffa dake Jamhuriyar Nijar. © REUTERS/Joe Penney
Talla

Mayakan sun kai farmakin ne a kusa da Ngouboua da ke yankin Tafkin Chadi da ya hada kasar da Nijar da Najeriya da Kamaru wadanda ke fama da rikicin Boko Haram da kuma ISWAP.

Mai magana da yawun fadar shugaban kasar ta Chadi, Brah Mahamat ya ce, an girke sojojin ne a tsibirin Bouka-Toulloroom, amma mayakan Boko Haram suka far musu.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce, sojoji 10 ne suka kwanta dama, amma wani jami’i da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP cewa, sojojin da suka mutu sun kai 30 , sannan kuma maharan sun yi awon gaba da kayayyakin aikinsu da suka hada da manyan makamai a cewarsa.

Jami’in wanda ya roki a boye sunan nasa, ya kuma kara da cewa, sojojin Chadi 150 ne aka girke a Bouka-Toullorom bisa umarnin shugaban kasa Mahamat Idriss Deby Itno kuma ba su jima da isa tungar ba.

A wata ziyara da ya kai yankin Tafkin Chadi a farkon wannan wata, shugaba Mahamat Deby  ya ce, mayakan masu da’awar jihadi ba su da sauran karsashin kaddamar da farmaki kan sansanin sojoji, abin da ya sa suka karkata hankalinsu ka fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.