Isa ga babban shafi

Makaman yakin Rasha da Ukraine na kwarara zuwa Tafkin Chadi - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar ana karkata wasu makaman da ake amfani da su a yakin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraine zuwa Yankin Tafkin Chadi. 

Shugaba Buhari kenan tare da wasu shugabannin kasashen Afirka
Shugaba Buhari kenan tare da wasu shugabannin kasashen Afirka © rfi
Talla

Buhari yace ya zama wajibi shugabannin dake yankin su tashi tsaye wajen daukar matakan da suka dace na dakile safarar kanana da manyan makaman dake kwarara zuwa yankin. 

Shugaban yace babu tantama yakin Rasha da Ukraine tare da wasu tashe tashen hankulan dake ake fama da su a yankin Sahel sun taimaka wajen rura wutar rikicin Boko Haram a Tafkin Chadi. 

Buhari yace duk da yake kasashen dake yankin sun yi kokari wajen dakile kaifin book haram da wasu kungiyoyi makamanta ta a yankin, har yanzu ana fuskantar barazanar yan ta’adda. 

Shugaban wanda ya yaba da rawar da rundunar hadin kai ta kasashen guda 4 ke takawa wajen murkushe mayakan book haram, ya bukace sojojin da su kara kaimi wajen fadada nasarorin da suke samu na kawar da duk wata barazanar da kasashen yankin ke fuskanta. 

Buhari ya kuma bukaci kasashen Tafkin Chadin da su tashi tsaye wajen gudanar da ayyukan raya kasa wadanda zasu inganta rayuwar jama’ar su da kuma kare lafiyarsu. 

Saboda haka shugaban ya bukaci aiwatar da shirin gina yankunan da aka kwato daga hannun mayakan book haram cikin gaggawa tare da samar da tsaro da kuma kayan more rayuwa. 

Babban Sakataren dake kula da Hukumar Tafkin Chadi Ambasada Mamman Nuhu yace Najeriya t abada kudin da ya zarce Dala miliyan 209 domin gudanar da ayyukan rundunar sojin hadin kan daga shekarar 2015 zuwa 2021. 

Shugabannin da suka halarci taron sun hada da shugaban Nijar Bazoum Mohammed da shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby da shugaban Benin Patrice Tallon da shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Fautin Archange Touadera da shugaban majalisar rikon kwaryar Libya Mohammed al Menfi. 

Taron shugabannin ya amince da shirin kaddamar da gidauniya domin bunkasa tafkin Chadi da fadada aikin janyo ruwa domin bunkasa Tafkin Chadi da bunkasa aikin samar da wutar lantarki a kogin Chari da Logone. 

Shugabannin sun kuma amince da bai wa Ambasada Mammane Nohou sakataren Hukumar Tafkin Chadi wa’adi na biyu na shekaru 4 wanda zai fara aiki daga ranar 15 ga watan Maris na wannan shekarar, tare da zaben shugaban kasar Chadi Mahamat Idis Deby a matsayin sabon shugaban kungiyar kasashen 4. 

Shugabannin sun kuma jinjinawa sojojin rundunar hadn gwiwa akan nasarar da suke samu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.