Isa ga babban shafi

Kamaru ta jibge Sojoji a Iyakarta da Najeriya saboda rikicin 'Yan ta'adda da Makiyaya

Gwamnatin Kamaru ta sanar da girke tarin dakarun Soji akan iyakarta da Najeriya bayan rikicin da aka samu tsakanin ‘yan awaren kasar da makiyaya daga makwabciyartata da ya kai ga kisan mutane 12. 

Sojojin Kamaru a yankin 'yan aware na Arewa maso Yamma.
Sojojin Kamaru a yankin 'yan aware na Arewa maso Yamma. © AFP - STRINGER
Talla

Sojoji fiye da 100 mahukuntan na Kamaru suka sanar da girkewa a yankin na Menchum da ke kan iyakar kasar da Najeriya don kwantar da hankula bayan rikici tsakanin ‘yan awaren da Fulani makiyaya. 

Abdoulahi Aliou, babban jami’in gwamnatin Kamaru mai kula da yankin na Gayama ya ce tun farko ‘yan awaren suka fara kashe makiyaya 2 saboda da kin biyansu wani harajin da suka gindayawa musu gabanin basu damar gudanar da harkokinsu na kiwo a yankin. 

Kashe 'Yan aware 4

A cewar jami’in bayan kisan mutane biyun ne Fulanin Makiyaya suka koma gida tare da shiryowa kai farmaki kan ‘yan awaren, tare da kashe 4 daga cikinsu.

Bayanai sun ce cikin fararen hula 6 da rikicin ya rutsa da su, har ta kai ga sun rasa rayukansu akwai mai garin Munkep da dan shi guda. 

An dai bayyana Fulanin a matsayin tsiraru da ke garin na Gayama. 

Yayin rikicin wanda ya faru cikin kwanaki 6 da suka gabata bayanai sun ce akwai fararen hula akalla 20 da suka jikkata yayinda aka rushe tarin gidaje baya ga shanu da dama da ‘yan awaren suka kashe.    

Tserewar jama'a

Majami’ar Katolika da ke Menchum ta ce tarin fararen hula sun tserewa garin na Gayama da sauran kauyukan makwabta don kaucewa cutuwa daga fadan tsakanin ‘yan awaren da Makiyaya da kuma yanzu da dakarun Soji suka shiga shiga garin. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.