Isa ga babban shafi

Senegal ta kame hodar Iblis fiye da kilogiram 800 a kan ruwa

Sojin ruwan Senegal sun sanar da kwace hodar Iblis mai nauyin kilogiram 805 yayin wani sumame akan ruwa cikin makon da ya gabata.

Hodar Iblis.
Hodar Iblis. © Corentin Charles / AP
Talla

Mahukuntan Senegal da ke sanar da kame jirgin dauke da hodar iblis din basu bayar da cikakken bayani kan mutanen da ke cikin jirgin ko kuma inda suka nufa ba.

Ko a watan Oktoban da ya gabata sai da hukumar kwastam ta kasar ta kame kilogiram 300 na hodar Iblis da darajar kudinsa ya kai yuro miliyan 37 makare a wata tanka da ta fito daga Mali.

Tsawon shekaru kenan yankin tsakiya da yammacin Afrika na ci gaba da kasancewa mashigar kwayoyi wadanda ake safararsu daga Latin Amurka.

Wani rahoto da Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai yaki da safarar miyagun kwayoyi UNODC ya fitar a bara ya bayyana yadda yankin a zama matattarar miyagun kwayoyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.