Isa ga babban shafi

Deby na Chadi ya gana da Netanyahu a Isra'ila domin gyara hulda da Yahudawa

Shugaban rikon kwaryar sojin Chadi Mahamat Deby ya gana da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu jiya Laraba domin karfafa alakar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby tare da Franministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yayin ziyara a Isra'ila. 01/02/23
Shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby tare da Franministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yayin ziyara a Isra'ila. 01/02/23 © Benjamin Netanyahu Twitter
Talla

Mahamat Deby ya ziyarci Isra'ila ne domin bude ofishin jakadancin kasar da ke tsakiyar Afirka a kasar yahudawa, bisa alakar diflomasiyya da suka kafa shekaru biyar da suka gabata.

A shekarar 2019, dai dai wa'adin karshe na Netanyahu, shi da marigayi shugaba Idriss Deby Itno, mahaifin Mahamat Deby, suka sanar da sake kulla huldar diflomasiyya.

A shekarar 2021 aka kashe Idris Deby wanda ya mulki Chadi fiye da shekaru talatin a fagen daga a yakin da yake yi da 'yan tawaye, inda dansa ya maye gurbinsa a matsayin shugaban kasa a gwamnatin mulkin soja.

Mahamat Deby wanda ya isa Isra’ila cikin daren Talataya samu tarba daga, shugaban Mossad David Barnea. Daga nan ne tawagar ta Chadi ta nufi hedikwatar Mossad da ke Glilot domin gudanar da wani taron biki.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.