'Yan sanda a Senegal sun fitar da jagoran 'yan adawa daga motarsa da karfi
Bayanai daga Senegal na cewa ‘yan sanda sun fasa gilasan babban madugun 'yan adawa Ousmane Sonko tare da tilasta masa fita daga motar sam jim kadan bayan bayyanar sa daga kotu.
Wallafawa ranar:
Hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta da Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya gani sun nuna yadda 'yan sanda suka fito dan siyasar mai shekaru 46 daga kujerar bayan motar, kafin daga bisani suka yi masa rakiya zuwa gidansa sai dai kakakin gwamnati ya musanta cewa an kama shi.
Ana dai tuhumar Sonko da laifin cin mutuncin jama'a, da bata suna, zargin da ya biyo bayan Wanda aka ya yi wa ministan yawon bude ido na Senegal a wani taron manema labarai a karshen shekarar da ta gabata.
Rahotanni sun ce jim kadan bayan fitowar daga kotun ya gaisa da magoya bayan sam dai-dai lokacin da ‘yan sanda suka fara harba hayaki mai as hawaye.
Ousmane Sonko dai ya shiga bakin littafin gwamnatin kasar tun a shekarar 2011, lokacin da ya nuna adawar sa ga gwamnatin Macky Sall.
Wannan sabuwar tuhuma dai na zuwa ne, bayan wadda aka yi massa ta fyade, laifin da idan aka tabbatar da shi zai shafe shekaru 10 a gidan yari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu