Isa ga babban shafi

Tsaffin ma'aikata a rundunar Barkhane sun roki Mali ta samar musu aiki

‘Yan kasar Mali da ke aiki da dakarun Faransa na Barkhane sun bukaci taimakon samun abin yi daga hukumomin rikon kwaryar kasar sakamakon kammala janyewar sojojin na Faransa daga kasar a cikin watan Agustan shekarar 2022, saboda tsamin dangantaka tsakanin Paris da Bamako. 

Mayakan rundunar Barkhane a Mali.
Mayakan rundunar Barkhane a Mali. AFP - THOMAS COEX
Talla

A cikin wata wasika da suka aikewa Firaministan kasar Mali Choguel Maiga tsoffin ma’aikatan na Barkhane sun roki hukumomi da su kawo musu dauki saboda sun rasa aikin yi kuma suna fuskantar wariya a kasar. 

Cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Fabarairu, kungiyar tsoffin ma’aikatan ta koka kan cewa mambobinta na cikin matsin tattalin arziki, “tun bayan ficewar rundunar Barkhane da ke taimakawa Mali yaki da ta’addanci, ta yadda basa iya biyan bukatun yau da kullum na iyalansu, inda ta roki Maiga da ya taimaka musu su samu aikin yi. 

Wadannan tsoffin ma'aikata da aka kiyasta yawansu ya kai 400 zuwa 450 da ke aiki a babban sansanin Barkhane da ke Gao a arewacin Mali da wasu sansanoni har da Bamako basa aiki karkashin sojojin Faransa kai tsaye, sun kasance karkashin wasu kamfanonin daukar ma'aikata na Mali. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.