Isa ga babban shafi

'Yan sandan Kenya sun kama masu zanga-zanga fiye da 200

‘Yan sandan Kenya sun ce wani  dalibin jami’a ya rasa ransa, yayin da kuma suka kama mutane fiye da 200, daga cikin dubban ‘yan kasar cikinsu har da wasu ‘yan majalisa 4, wadanda ke zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba William Ruto da suke zargi da gazawa wajen magance matsalar tattalin arzikin da ta haifar da tsadar rayuwa a kasar.

Daya daga cikin masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Kenya, yayin da ya dage wajen jifan 'yan sanda.
Daya daga cikin masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Kenya, yayin da ya dage wajen jifan 'yan sanda. AP - Ben Curtis
Talla

Rahoton ‘yan sanda ya nuna cewar dalibin da aka kashe, dan jami’ar Maseno da ke yammacin Kenya ne, wanda ya rasa ransa bayan da jami’an tsaro suka harbe shi a wuya yayin arangamar da suka yi da masu zanga-zanga.

Jami’an tsaron sun ce abokan aikinsu akalla 24 ne suka  jikkata yayin arrangama da masu  boren.

Dubun dubatar ‘yan kasar ta Kenya sun shiga-zanga-zangar ce bayan amsa kiran jagoran ‘yan adawa Raila Odinga.

Wannan dai shi ne karo na farko da aka samu barkewar tashin hankali a kasar Kenya da ke gabashin Afirka, tun bayan da Ruto ya hau karagar mulki watanni shida da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.