Isa ga babban shafi

Kenya za ta harba tauraron dan adam na farko

Kasar Kenya za ta harba tauraron dan adam na farko a yau Litinin, inda jirgin ‘yan saman jannatin mai suna Taifa-1 zai tashi a cikin rokar Falcon 9 na SpaceX daga sansanin sojojin sararin samaniya na Vandenberg a California.

Wani tauraron dan adam da kasar Indiya ta harba, ranar 22 ga watan Yulin 2019.
Wani tauraron dan adam da kasar Indiya ta harba, ranar 22 ga watan Yulin 2019. AP
Talla

Tauraron dan Adam din, wanda injiniyoyin kasar Kenya suka kera, ana sa ran zai samar da muhimman bayanai kan noma, da samar da abinci, da sauran fannonin da za su tallafawa tattalin arzikin kasar.

Harba jirgin wani muhimmin ci gaba ne ga shirin sararin samaniyar kasar Kenya, kuma ma'aikatar tsaron kasar da hukumar kula da sararin samaniyar kasar Kenya sun bayyana shi a matsayin wata muhimmiyar nasara ga al'ummar kasar.

An kera tauraron dan adam din ne tare da hadin gwiwar wasu kwararru da ke kula da hartkokin sararin samaniya a kasar Bulgaria.

Kasar Kenya wadda ke da karfin tattalin arziki a gabashin Afirka, na fama da fari mafi muni a cikin shekaru da dama bayan rashin samun ruwan sama tsawon shekaru biyar a jere.

Don haka, ana sa ran shirin harba tauraron dan adam din zai taimaka sosai wajen samar da bayanai kan yadda za a tallafawa shirye-shiryen samar da abinci a kasar.

Kaddamar da nasarar da aka samu wani bangare ne na wani gagarumin yunkuri da kasashen Afirka ke yi na kirkire-kirkiren kimiyya da bunkasa shirye-shiryen sararin samaniya.

Ya zuwa shekarar 2022, akalla kasashen Afirka 13 ne suka kera tauraron dan adam 48, said ai babu wanda aka kaddamar daga nahiyar, said ai a wasu kassashen Turai, a cewar Space in Africa.

Masar ita ce kasa ta farko a Afirka da ta aika da tauraron dan adam zuwa sararin samaniya a shekarar 1998, kuma a cikin 2018, Kenya ta harba nanosatellite na farko na gwaji daga tashar sararin samaniya ta kasa da kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.