Isa ga babban shafi

Kamaru za ta karfafa tsaron kan iyakokinta da Najeriya da Afirka ta Tsakiya

Rundunar sojin kamaru na shirin tura karin dakarun ta kan iyakokin kasar da Najeriya da kuma jamhuriyar Afirka ta tsakiya, a yayin da ake cigaba da fuskantar hare hare daga mayakan Boko Haram na ‘Yan tawaye. 

Wata rundunar soji da Kamaru ta jibgi a kan iyakarta da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekarar 2014.
Wata rundunar soji da Kamaru ta jibgi a kan iyakarta da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekarar 2014. FP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

Dakarun na kamaru sun bayyana cewa akwai daruruwan ‘yan kungiyar Boko haram dake boye a cikin daji dake iyakokin, bayan da akai musu mamaya a yankin Mayo Moskota dake kan iyakar kasar da Najeriya. 

Gwmanatin kasar ta kamaru dai ta bayyana cewa an kona gidaje da dama abin da yabar tulin mutane suka rasa matsugunan su. 

Dangane da wannan matsalar ce ministan tsaron kasar Joseph Beti Asomo ya sanar da cewa shugaban kasar Paul Biya ya bukaci a hanzarta ganawar gaggawa don shawo kan wannan matsalar tsaron dake neman jefa kasar cikin halin kaka nika yi. 

Afirka ta Tsakiya

Yayin da za’a tura tarin sojoji dukkanin sabbin wuraren da ake samun matsalar kai hare hare, daga ‘Yan aware a yankunan renon Ingilishi da kuma ‘yan tawaye a kan iyakar kasar da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. 

Gwamman ta kuma sanar da shirin horas da matasa dubu uku dabarun yaki nan da watanni 20 masu zuwa domin taimakawa sojoji kawo karshen matsalolin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.