Isa ga babban shafi

Mutane 127 sun mutu a ambaliyar ruwa a Ruwanda

Mutane akalla 127 ne aka tabbatar da mutuwarsu a Ruwanda, sannan an samu dimbin asarar dukiya sakamakon ambaliyar ruwa tare da zabtarewar kasa da aka samu a yankunan arewaci da yammacin kasar.

Hukumar kula da yanayi ta kasar na danganta irin ambaliyar ruwan da ake yi a Ruwanda a shekarun baya-bayan nan da sauyin yanayi.
Hukumar kula da yanayi ta kasar na danganta irin ambaliyar ruwan da ake yi a Ruwanda a shekarun baya-bayan nan da sauyin yanayi. AFP - PETER LOUIS
Talla

Hukumomi a kasar sun bayyana cewa ana sa ran adadin wadanda suka mutun zai karu yayin da ambaliyar ruwan ke ci gaba da karuwa.

Ministar Agajin Gaggawa ta kasar Mary Solange ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarun Faransa cewa tuni ma'aikatan ceto suka bazu a yankunan da lamarin ya faru domin ceto wadanda gini ya rufta akansu tare da agaza wa wadanda suka rasa muhallansu.

Ruwanda ta yi fama da mamakon ruwa a tsakanin watan Maris da Afirilu wanda ya haifar dinbin hasara na rayuka da dukiya, amma hukumomi a kasar sun ce ruwan saman da aka yi a daren ranar Talata ya kazanta.

Wannan shi ne ambaliya mafi muni da aka gani a Rwanda tun watan Mayun 2020 inda mutane kusan 80 suka mutu.

Hukumar kula da yanayi ta kasar na danganta irin ambaliyar ruwan da ake yi a Runda a shekarun baya-bayan nan da sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.