Harin ta'addanci ya yi sanadin mutuwar manoma 33 a Burkina Faso
A Burkina Faso, akalla mutane 33 ne suka mutu bayan da ‘yan bindiga suka bude wuta a kan wasu manoma a yankin yammacin kasar da ke fama da rikicin ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi, kamar yadda gwamnan yankin ya bayyana a jiya Asabar.
Wallafawa ranar:
Gwamnan, Babo pierre Bassinga ya bayyana a wata sanarwa cewa harin ya auku ne a kauyen Youlou a yammacin Alhamis da misalin karfe biyar na yamma agogon GMT.
Majiyoyi masu karfi daga yankin sun ce , ‘yan bindigar da suka zo a kan babura, sun afka wa manoma fararen hula ne, wadanda ke noma a gefen kogi, inda suka yi musu harbin kan mai uwa da wabi.
A ranar Juma’a aka binne wadanda lamarin ya rutsa da su.
Rahotanni sun ce wasu mutane 3 sun samu munanan raunuka sakamakon harbin bindiga, kuma maharan sun kona wasu kadarori kafin su fara harbe-harbe.
Harin na ranar Alhamis din na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da aka tsinci gawar wani babban jami’i a yankin Boucle dun Mouhoun a cikin wani kungurmin daji.
Rikicin ta’addanci a Burkina Faso ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 10 tare da daidaita miliyan 2.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu