Isa ga babban shafi

Sojin Sudan sun janye daga tattaunawar sulhun da Saudiya ke jagoranta

Gwamnatin Sojin Sudan ta janye daga tattaunawar sulhun da kasashen Saudiya da Amurka ke jagoranta a kokarin shawo kan rikicin kasar na kusan watanni biyu, janyewar da ke zuwa bayan sojin sun zargi dakarun RSF da karya dokokin tsagaita wutar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu a makamanciyar tattaunawar.

Wasu sojojin Sudan karkashin jagoranci Abdel Fattah al-Burhan.
Wasu sojojin Sudan karkashin jagoranci Abdel Fattah al-Burhan. © Forces armées soudanaises / via Reuters
Talla

Gwamnatin Sojin ta Sudan karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan ta ce dakarun na RSF karkashin jagorancin Mohamed Hamdan Daglo sun ki mutunta matakan da aka cimma karkashin yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakaninsu, wannan dalili ya sanya ta ganin rashin amfani ci gaba da tattaunawar don sasanta rikicin.

Wakilicin gwamnatin ta Sudan a Jedda, ya bayyanawa zaman taron cewa mayakan RSF basu janye daga asibitoci da makarantu da kuma matsugunan fararen hula ba, duk da cimma yarjejeniyar tsagaita wutar mako guda da kuma kara wa'adin zuwa kwanaki 5.

Zaman taron na jiya, da ya yi fatan ci gaba da tsawaita yarjejeniyar don sulhunta rikicin na Sudan, ya koka da matakan da RSF ke dauka da ke ci gaba da cutar da dimbin fararen hular da yaki ya daidaita a sassan kasar.

Majiyoyi sun bayyana cewa duk da matakin tsawaita yarjejeniyar har zuwa talatar makon nan an ci gaba da ganin hare-hare daga bangarorin biyu da ke farmakar juna a ciki da wajen birnin Khartoum da kuma yammacin Darfur.

A lokuta da dama dai Saudiya na koka da yadda kowanne bangare ke ci gaba da jan tunga tare da ganin lallai zai iya nasara a yakin, dalilin da kasar ke cewa shi ne ya hana samun galaba wajen sasanta rikicin kasar ta arewacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.