Isa ga babban shafi

Kwamitin hadin gwiwa na Libya ya rattaba hannu kan yarjejeniyar dokar zabe

Wakilan kwamitin da ke shirya zaben Libya, sun sanar da cewa, sun cimma matsaya kan dokokin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar, inda suke dakon shugabannin majalisar wakilai da na majalisar dokokin kasar su rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Wani mutum dauke dda kwalin da ke neman a yi zabe, a zanga-zangar neman a gudanar da zaben kasar.
Wani mutum dauke dda kwalin da ke neman a yi zabe, a zanga-zangar neman a gudanar da zaben kasar. REUTERS - ESAM OMRAN AL-FETORI
Talla

A wata ganawa da manema labarai daga Bouznika na kasar Morocco, shugaban tawagar kwamitin, Jalal Al-Shuwaidi, ya bayyana cewa, sun kammala tsara dokokin zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin kasar a majalisunsa biyu.

Al-Shuwaidi ya tabbatar da cewa kwamitin ba ya fuskantar matsin lamba ko tsoma baki daga Maroko ko kuma daga ketare, yana mai mika godiyarsa ga Masarautar Morocco bisa karbar bakuncin tarukan kwamitin a cikin kwanaki goma da suka gabata, da kuma godiya ga kokarin da take yi na tallafawa kasar Libya.

Shi ma shugaban tawagar bangaren zartaswa a kwamitin Omar Boulifa, ya yi nuni da cewa, dokokin da kwamitin ya amince da su, sun ba kowa damar tsayawa takara, kuma ba su kebe kowa daga shiga zaben ba.

Boulifa ya bayyana cewa, an kammala dukkan batutuwan da suka sa a gaba kuma an amince da su, an kuma amince da dokar zaben 'yan majalisar dokokin kasar da na shugaban kasa, kuma an sanya hannu kan duk wani abin da suka cimma bisa ra'ayin Libya.

Ministan harkokin wajen kasar Morocco Nasser Bourita ya bayyana cewa, taron ya kasance mai nuna kishin kasa, kuma ya yi aiki wajen samar da ra'ayin ci gaban kasar ta Libya.

Bourita ya kara da cewa, 'yan kasar Libya sun tabbatar da cewa, idan aka ba su dama, za su iya cimma matsaya guda tare da gudanar da zabe, yana mai jaddada cewa taron kwamitin wani muhimmin mataki ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.