Isa ga babban shafi

Kungiyoyin 'yan ta'adda sun ta'azzara safarar muggan kwayoyi a Sahel-MDD

Hukumar yaki da muggan kwayoyi ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan hodar ibilis da ake kwacewa a yankin Sahel na yammacin nahiyar Afrika ya karu daga kilogram 13 a shekarar 2020 zuwa kilogram 863 shekaru 2 kacal bayan da kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin suka shiga harkar don neman kudaden shiga.

Masana sun ce yaanzu ta yankunan yammaci da jtsakiyar Afrika sun zama wata kafa ta shigowar hodar ibilis nahiyar.
Masana sun ce yaanzu ta yankunan yammaci da jtsakiyar Afrika sun zama wata kafa ta shigowar hodar ibilis nahiyar. AFP - JORGE GUERRERO
Talla

Wannan na kunshe ne a rahoton hukumar yaki da muggan kwayoyin na shekarar 2023, wanda a cikinsa ta ce an yi kame masu gwabi a shekarar da ta gabata, inda a Burkina Faso   aka kama kilo 488, Nijar kilo 213 sai Mali da aka kama kilo 160 na hodar ibilis din.

Hukumar ta ce adadin na iya zarta haka, duba da cewa ta yi amannar akwai da dama wadanda ba a kai ga kama sub a  yankin.

Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar sun shafe shekaru suna kokarin dakile ayyukan ta’addanci a kasashensu, wadanda suka hada da na ‘yan ta’adda masu alaka da kungiyar  Al-Qaeda da kuma ISIS.

Masana na kallon yaankuna  yammaci da tsakiyar Afrika a matsayin hanyoyin da ake bi wajen da hodar  ibils ke bi wajen shigowa kasar, inda a shekarun bayan nan  na samu karuwar masu ta’ammali da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.