Isa ga babban shafi

Yankin Sahel na bukatar kudaden yaki da masu tsattsauran ra'ayi- MDD

Babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da nahiyar Afrika Martha Pobee, ta koka da yadda yankin Sahel ke matsayin matattarar ayyukan ta'addanci sakamakon yadda ake ganin karuwar tashe-tashen hankula da ke da nasaba da masu tsattsauran ra'ayin addini bayan gazawar rundunar hadin gwiwa wajen yakar kungiyoyin 'yan ta'adda da ya ta'azzara rashin tsaro a yankin. 

Kungiyoyin 'yan ta'adda na ci gaba da karfi a kasashen yankin Sahel.
Kungiyoyin 'yan ta'adda na ci gaba da karfi a kasashen yankin Sahel. AFP - HO
Talla

Martha wadda ita ce mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da nahiyar Afrika, ta bayyana hakan ne a lokacin taron majalisar tsaro, wanda ya tattauna kan yadda za a yaki kungiyoyin ta’addanci da ke da alaka da kungiyar IS da al-Qaida. 

A shekarar 2014 ne aka samar da rundunar hadin gwiwa tsakanin kasashen Burkina Faso da Chadi da Mauritania da kuma Nijar, ganin cewa a shekarar da ta gabata Mali ta fice daga cikin wannan tafiya. 

Sai dai a cewar Pobee tun a watan Janairun da ya gabata, rabon da rundunar ta gudanar da wani gagarumin aiki, saboda kintsawa don tunkarar sabbin kalubalen da ke gaban ta, wanda ke da nasaba da rashin kudaden tafiyar da harkokinta kama daga yaki da 'yan ta'addan kai tsaye da kuma rage tsaurin akida tsakanin jama'ar yankin. 

A baya-bayan nan ne Burkina Faso da kuma jamhuriyar Nijar, suka sake inganta alakar su da Mali, don tunkarar kalubalen tsaro a iyakokin kasashen su. 

Jami'ar ta yi gargadin cewar rashin cimma wata jituwa tsakanin kasashen waje abokan huldar su ne ya sanya rundunar ta gaza samun gudunmuwar kudi don gudanar da ayyukan ta yadda ya kamata. 

Toh sai dai shugaban kungiyar kasashen G5 Sahel Eric Tiare, ya ce an kammala tsara sabbin shirye-shiryen yadda rundunar za ta rinka gudanar da aikin ta, wanda za a mikawa majalisar tsaro da kuma kungiyar tarayyar Afrika don amincewa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.