Isa ga babban shafi

Macron ya sanar da kawo karshen aikin rundunar Barkhane a Sahel

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya sanar da kawo karshen aikin rundunar Barkhane mai yaki da ayyukan ta’addanci a kasashen Sahel, matakin da ke zuwa kasa da watanni 3 bayan ficewar Sojin Faransar daga Mali.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. AP - Christian Hartmann
Talla

Macron wanda ya sanar da wannan mataki da tsakar ranar yau laraba, yayin gagarumin taron da ya jagoranta a birnin Toulon ya ce gwamnatinsa za ta fara aiki tare da abokan huldarta a Afirka domin sauya dabarun ayyukan sojojin Faransa kimanin dubu 3000 da suka rage a kasashen Nijar, Chadi da Burkina Faso, wanda kuma ba a sa ran adadinsu zai canja a nan kusa.

A jawabin na Macron wanda ya mayar da hankali kan sabbin dabarun da kasar za ta yi amfani da su don taimakawa kasashen na Afrika yaki da matsalolin tsaron da suka dabaibaye su, ya kuma jaddada muhimmancin alakar da ke tsakanin Faransar da kawayenta Jamus da Birtaniya duk da rikicin baya-bayan nan.

Macron ya bayyana cewa yana son amfani da damar taron wajen sanar da kawo karshen aikin rundar Barkhane a Sahel.

Haka zalika jawabin na Macron a taron na yau laraba ya kuma tabo tsaron sashen nukiliyar kasar baya ga bayyana matsayarsu kan ci gaba da mara baya ga Ukraine a mamayar da Rasha ke mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.