Isa ga babban shafi

Juyin mulkin a kasashen yankin Sahel yana taimakawa ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi

Masana sha’anin  tsaro da ke bibiyar lamurran da ke wakana a yankin Sahel, sun yi gargadin cewa, juyin mulkin da ake samu a wasu kasashen yankin yana taimakawa ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi ne, sabanin alkawuran da sojoji ke yin a kawo karshen hare-haren mayakan.

Dakarun wanzar da zaman lafiya  a yankin Mali
Dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin Mali © FLORENT VERGNES/AFP
Talla

Matsalar ta’addanci a yankin Sahel ta yi fara yin karfi ne tun daga shekarar 2012 a arewacin Mali, inda a shekarar 2015, hare-haren suka bazu zuwa yankin tsakiyar kasar, sai kuma sassan Nijar da Burkina Faso, lamarin da yayi sanadin lakume rayukan dubban mutane gami da tilastawa wasu fiye da miliyan 2 tserewa daga muhallansu.

A baya bayan nan ne dai sabuwar gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin Kaftin Ibrahim Traore, ta gudanar da juyin mulki karo na biyu a Burkina Faso cikin watanni 9 saboda gazawa wajen dakile hare-haren masu ikirarin jihadi, makamancin abinda ya auku a Mali a shekarun 2020 da 2021.

Yawaitar juyin mulkin dai ya zo ne a yayin da Faransa da Rasha ke takara kan neman tasiri a kasashen na yankin Sahel, wadanda suka karkata ga gwamnatin Vladimir Putin don samun taimako wajen yakar masu ikirarin jihadi.

Sai dai Yvan Guichaoua kwararre a Makarantar Nazarin lamurran Kasa da Kasa da ke Brussels ya ce juyin mulkin da sojoji ke yi a Sahel zai taimakawa 'yan ta’adda masu ikirarin jihadi ne da ke biyayya ga IS ko Al Qa’eda, kawai amma ba Faransa ko Rasha ba, domin kuwa bas a iya cika alkawuran da suka dauka na tabbatar da tsaro.

Shi ma dai Djallil Lounnas na Jami'ar Al-Akhawayn ta kasar Morocco ya ce juyin mulkin da sojoji ke yi a Sahel yana kassara tsarin tsaro kasashen da suke ne gami da haifar da rarrabuwar kai tsakanin sojoji, inda ake samun masu goyon bayan da kuma adawa da duk wani juyin mulki da ya gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.