Isa ga babban shafi

Sabon kundin tsarin mulkin Mali ya fara aiki a hukumace wannan Asabar

Shugaban mulkin sojin Mali ya shigar da sabon kundin tsarin mulkin kasar dake yammacin Afirka a wannan Asabar, wanda ya haifar da zanga-zangar da ‘yan adawa da kungiyoyin farar hula.

Shugaban sojin mulkin Mali yayin kada kuri'ur raba gardama
Shugaban sojin mulkin Mali yayin kada kuri'ur raba gardama © Colonel Assimi GOITA
Talla

Sabon kundin tsarin mulkin ya zama doka ne a lokacin da Kanar Assimi Goita, shugaban mulkin soji da ke mulki tun shekarar 2020 ya shiga da shiga da shi ofishinsa a hukumance ranar Asabar.

Shugabannin sojojin sun mayar da fasalta kundin tsarin mulkin kasar a matsayin wani ginshiki na sake gina kasar Mali, da ke fuskantar kungiyoyi masu ikirarin jihadi sauran rikice-rikice masu yawa.

Kashi 97 suka amince

Hukumar zaben Mali tace Kashi 97 cikin 100 na kuri'un raba gardama suka amincewa da sauya kundin tsarin mulkin a watan da ya gabata, sai dai kuma an ce kashi 38 cikin 100 na masu kada kuri'a ne suka fito runfunan zabe a kasar dake yankin Sahel mai fama da tashe-tashen hankula na tsawon shekaru 11.

An yi watsi da korafe-korafe da dama da aka shigar gaban kotun tsarin mulkin, ciki har da na neman a soke zaben raba gardama saboda ba a gudanar da shi a duk fadin kasar.

Kokarin Goita na ci gaba da mulki

Masu adawa da shirin na ganin an yi zaben ne domin ci gaba da rike kanar din bayan zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a watan Fabrairun 2024, duk kuwa da alkawarin da suka yi na mikawa farar hula bayan zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.