Isa ga babban shafi

An bude bukin wasannin Francophonie a Demokradiyyar Congo

A yau juma’a ne ake soma bukin wasannin kasashe masu amfani da harshen Faransanci karo na 9 da muka sani Francophonie a babban filin wasa na les Martyrs ko filin wasan Shahidai da ke birnin Kinshasa.

Wasannin Francophonie
Wasannin Francophonie © D.R.
Talla

'Yan kallo dubu tamanin ne ake sa ran za su halarci  faretin matasa 'yan wasa da masu fasaha dubu uku, daga kasashe kusan talatin, wadanda ke shiga gasar  da ke gudana na tsawon kwanaki goma a babban birnin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, birni mafi girma na masu magana da harshen Faransanci a duniya mai kimanin mutane miliyan goma sha biyar.

 

Baya ga faretin tawagogi na kasashe za a gabatarwa mutane da wani shiri na musamman wanda ya kumshi nuna hotuna dauke da sautuka da nufin nuna sauyin da aka samu a wannan kasa ta Congo,sanarwar da  kakakin gwamnatin kasar Patrick Muyaya ya sanar.

Francophonie
Francophonie © https://www.francophonie.org/

A shekara ta 2019  aka zabi kasar ta Congo a matsayin wacce za ta shirya wasannin,to sai dai bisa dalillai da aka sani a lokaci na rashin shiri da kuma bulluwar annobar Covid 19 an dage wasannin.

Ba za mu rufe labarin wasannin kasashe masu amfani da harshen faransanci ba ba tare da mu  duba wainar da ake tuyawa dangane da kasancewar Louise Mushikiwabo yar kasar Rwanda da ke rike da mukamin magatakardar kungiyar ta OIF,ganin kazamar halaka da ke tsakanin Rwanda da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo,inda kasashen biyu ke zargin junansu a lamarin da ya shafi rashin tsaro a yankin Kivu.

Babbban filin wasa na Stade des Marthyrs na DRCongo
Babbban filin wasa na Stade des Marthyrs na DRCongo © GUERCHOM NDEBO / AFP

A ranar litinin  farkon wannan makon ne gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta sanar da kasancewar  Louise Mushikiwabo, tsohuwar ministar harakokin wajen Rwanda ,sai dai mai magana da yawunta ya nuna washegari cewa ba za ta zo ba saboda ba a gayyace ta ba, wanda ma’aikaciyar hukumar ta OIF, Caroline St-Hilaire, wadda ta maye gurbinta a Kinshasa ta sake maimaitawa a ranar Laraba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.