Isa ga babban shafi

Harin masu tayar da kayar baya ya kashe sojojin kasar Mali da dama

Sojojin Mali da dama ne suka mutu a wani hari da sojojin suka dora alhakinsa kan masu tayar da kayar baya a yankin Menaka da ke arewa maso gabashin kasar.

Dakarun tsaron Mali kenan, da suka taso keyar wani dan kunar bakin wake a babban masallacin Bamako ranar 20 ga watan Yulin 2021.
Dakarun tsaron Mali kenan, da suka taso keyar wani dan kunar bakin wake a babban masallacin Bamako ranar 20 ga watan Yulin 2021. AFP - EMMANUEL DAOU
Talla

Sanarwar da gwamnatin sojin kasar ta fitar ta ce, yan ta’addan sun yi asarar akalla mayaka 15.

Wani jami'in yankin ya ce wadanda suka bata da kuma jikkata sun kai mutum 20 bayan harin na ranar Alhamis wanda aka yi wa gungun sojojin kwanton bauna, yayin da suke rakiyar manyan motoci zuwa makwabciyar kasar Nijar, wadda take fuskantar takunkumi, sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a makon jiya.

Kasar Mali da ke karkashin mulkin soja bayan juyin mulkin shekarar 2020, ta goyi bayan juyin mulkin Nijar tare da gargadin cewa za ta dauki duk wani matakin soji daga wajen kasar a matsayin shelanta yaki.

Wani dan majalisar mulkin sojan Nijar ya jaddada a ziyarar da ya kai a birnin Bamako ranar Laraba muhimmancin hadin gwiwa tsakanin jihohin biyu da ke makwabtaka da su domin fuskantar hare-haren masu tayar da kayar baya.

Arewacin Mali dai na fama da tashe-tashen hankula tun a shekara ta 2012, kuma tashe tashen hankulan sun bazu zuwa yankunan tsakiya da kuma makwabtan kasashe wato, Burkina Faso da Nijar.

Yankin Menaka dai ya shafe watanni yana fama da matsalalolin hare-hare masu alaka da kungiyar IS ke yi a yankin sahara.

Rahoton Human Rights Watch na baya-bayan nan ya zargi kungiyar da laifin kashe daruruwan mutane, tare da tilastawa dubbai barin gidajensu tun farkon wannan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.