Isa ga babban shafi

Human Rights Watch na zargin sojojin Mali da yi wa fararen hula kisan gilla

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights ta zargi sojojin Mali da wasu takwarorinsu na ketare da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar da kashe fararen hula da dama, da sunan yaki da yan ta’adda masu ikirarin jihadi 

Wasu sojojin Mali yayin atisaye a yankin Menaka da ke arewa maso gabashin kasar.
Wasu sojojin Mali yayin atisaye a yankin Menaka da ke arewa maso gabashin kasar. © AFP PHOTO / Etat Major des Armees
Talla

 

Human rights Watch ta ce sojojin da ake kyautata zaton na kamfanin Wagner ne, sun fara cin zarafin jama’a tun karshen shekarar 2022, lokacin da dakarun tare da hadin gwiwar na kasar Mali ke aikin kakkabe ‘yan ta’adda a sassan kasar 

Haka kuma kungiyar ta zargi sojojin da azabtarwa da kullewa da kuma sace kayayakin fararen hula. 

Kungiyar ta cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce sojojin na Wagner sun kashe mutane da gangan tare da tilastawa wasu da dama barin muhallansu. 

Wannan ce ta sanya kungiyar ta kare hakkin dan adam ta bukaci kungiyar tarayyar Afirka da ta yi duk mai yiwuwa wajen dakile cin zarafin da ake yi wa al’ummar Mali da sunan basu kariya ko kuma yaki da ta’addanci, sanan ta kama mahukuntan kasar ta Mali da laifin. 

Wannan zargi na Human Rights Watch ya biyo bayan rahoton da ta wallafa a game da karuwar kisan fararen hula da yi wa mata fyade da kuma satar kayan jama’a  duk a kasar ta Mali.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.