Isa ga babban shafi

'Yan tawayen Mali na barazanar ficewa daga yarjejeniyar zaman lafiyar kasar

‘Yan tawayen Mali da suka kulla yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin kasar a shekarar 2015 sun janye wakilcinsu daga birnin Bamako lamarin da ya sanya fargabar fuskantar sabon rikici tsakaninsu da Sojojin da ke mulkin kasar a yanzu.

Shugabancin kungiyar 'yan tawayen na kabilar Toureg.
Shugabancin kungiyar 'yan tawayen na kabilar Toureg. REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

Guda cikin jagororin ‘yan tawaye kabilar ta Tuaregs karkashin kungiyar ci gaban al’ummar Azzawad da ake kira CMA ya tabbatar da janye wakilcinsu daga fadar gwamnatin ta Mali, saboda dalilai na rashin tabbas da ya sanya jagorancinsu na kasa kiran wakilcin da ke birnin na Bamako.

Attaye Ag Mohamed da ke jagorancin wakilcin na CMA a Bamako ya shaidawa AFP cewa jagorancin kungiyar ya yi imanin cewa basu da cikakken tsaro ko makoma a birnin na Bamako haka zalika an sauka daga turbar dalilan da suka kawo su fadar ta Mali.

Duk da yadda Sojojin da ke mulkin Mali ke ci gaba da nanata cewa za su ci gaba da mutunta yarjejeniyar ta 2015, amma kungiyar ta Azzawad ko kuma CMA na ganin matakin garambawul ga kundin tsarin mulkin kasar ta Mali da Sojin suka jagoranta ya yi karantsaye ga yarjejeniyar da suka cimma, batun da ya haddasa takun saka tsakaninsu tun watan Yunin da ya gabata.

Wannan takun saka dai ya sanya fargabar yiwuwar sake daukar makaman kungiyar wadda ta faro tawaye da makami a shekarar 2012 gabanin mayaka masu ikirarin jihadi su karbe ragamar tawayen daga hannunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.