Isa ga babban shafi

Mali da Aljeriya za su sabunta yarjejeniyar zaman lafiya ta 2015

Kasar Mali da makwabciyarta Aljeriya na fatan sake farfado da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a shekarar 2015 tsakanin Bamako da 'yan tawayen arewacin Mali wanda a yanzu ke cike da rudani, lamarin da ke kara nuna fargabar sake barkewar rikici.

Bilal Acherif kenan, babban sakataren kungiyar fafutukar 'yantar da Azawad na kasar Mali, a lokacin yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Mali da wasu kungiyoyin masu dauke da makamai a arewacin kasar, an dauki hoton, ranar 1 ga Maris, 2015 a Algiers babban birnin kasar Aljeriya. Yarjejeniyar wacce aka shafe watanni takwas ana tattaunawa, ta tanadi mika ragamar mulki daga Bamako zuwa arewacin kasar, yanki mai girman Texas da 'yan tawayen ke kira Azawad.
Bilal Acherif kenan, babban sakataren kungiyar fafutukar 'yantar da Azawad na kasar Mali, a lokacin yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin Mali da wasu kungiyoyin masu dauke da makamai a arewacin kasar, an dauki hoton, ranar 1 ga Maris, 2015 a Algiers babban birnin kasar Aljeriya. Yarjejeniyar wacce aka shafe watanni takwas ana tattaunawa, ta tanadi mika ragamar mulki daga Bamako zuwa arewacin kasar, yanki mai girman Texas da 'yan tawayen ke kira Azawad. AFP PHOTO / FAROUK BATICHE
Talla

Yarjejeniyar dai na da nufin kwantar da tarzoma a yankin da ta barke a shekarar 2012 lokacin da 'yan kabilar Abzinawa suka tayar da kayar baya ga gwamnatin kasar.

Masu tayar da kayar baya sun matsa kaimi, daga bisani kuma suka shiga cikin tsakiyar Mali, Nijar da Burkina Faso, inda suka kashe dubban mutane tare da tilastawa miliyoyin mutane barin gidajensu.

Yarjejeniyar ta 2015 ta hada 'yan tawayen Abzinawa da kuma gwamnatocin yanki, tare da karin 'yancin cin gashin kai da kuma damar shigar da mayaka cikin rundunar cikin dakarun gwamnati domin yin aiki tare a yankin.

Sai dai an aiwatar da wani bangare ne kawai a yarjejeniyar abin da ya fusata 'yan tawayen suka fice daga ciki.

A wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar, kasashen Mali da Aljeriya sun ce suna son sake kulla yarjejeniyar.

Ministan Harkokin Wajen Aljeriya Ahmed ya ce bayan tattaunawa da shugaban mulkin sojan kasar, Kanar Assimi Goita ya ce sun gudanar da cikakken bincike kan abubuwan da ake bukata don tabbatar da sake gudanar da aiki tare.

Ziyarar tasa na zuwa ne bayan da tsaffin 'yan tawayen Mali suka ziyarci Algeria a watan Fabrairu domin tattaunawa kan yadda za a kawo karshen rikicin.

Wata babbar kungiyar 'yan tawayen da ta rattaba hannu kan yarjejeniyar ta 2015 ta mayar da martani game da fatan ganin an dawo da yarjejeniyar kan turba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.