‘Yan sanda tara ne aka kashe a wani harin kwanton bauna a Somaliland
A Somaliland an kaiwa ‘yan sanda 9 harin kwanton bauna tare da kashe su bayan wata musayar wuta da aka yi,yankin da ya ayyana ‘yancin kai a Somaliya.
Wallafawa ranar:
Lamarin ya faru ne tsakanin jami’an tsaro da ‘yan tawaye masu dauke da makamai a jiya Juma'a a wani yanki mai tsaunuka mai tazarar kilomita 95 daga babban birnin yankin Hargeysa, in ji kwamandan 'yan sanda Mohamed Adan Saqadhi.
'Yan bindigar "sun yi wa 'yan sanda 30 kwantan bauna kuma sun kashe tara", in ji Saqadhi, ya kara da cewa 'yan sanda 17 sun jikkata.
A shekarar 1991 wani tsohon yanki na Birtaniya, Somaliland ya ayyana kansa a matsayin yanki mai cikkaken ‘yancin kai daga Somaliya, yayin da wannan kasa ta fada cikin rudani da har yanzu ta kasa kawo karshen sa.
Tun a watan Yuli ne mahara suka dauki makamai domin nuna adawa da karin wa'adin da shugaban kasar Somaliland, Muse Bihi Abdi ya yi a watan Oktoban da ya gabata. Hukumar zaben Somaliland ta sanar a watan da ya gabata cewa za a gudanar da zabe zaben shugaban kasa a watan Nuwamba na shekarar 2024 , watanni 11 bayan zaben fidda gwani na jam'iyyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu