Isa ga babban shafi

Fararen hula 6 suka mutu a harin da Al-Shebaab ta kai wani otel a Mogadishu

Rundunar ‘yan sandan Somalia ta bayyana mutuwar  fararen hula 6  da jikkatar wasu 10, sakamakon harin da mayakan Al-Shabaab suka kai tare da mamaye wani otel da ke gefen gabar teku a Mogadishu babban birnin kasar kasar, inda suka kwashe  sa’o’i 6.

Wasu daga cikin mayakan al-shebaab
Wasu daga cikin mayakan al-shebaab REUTERS/Feisal Omar
Talla

 

Harin wanda kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakinsa, tun da misalin karfe 8:00 na daren ranar Juma’a ne wasu maharanta bakwai suka kai shi otal din Pearl Beach, wani shahararren wurin da ke gabar tekun Liido da ke Mogadishu.

Kuma har sai da misalin karfe 2:00 na safe, aka kawo karshen kawanyan da suka yi wa Otel din, bayan wani kazamin musayar wuta da aka yi tsakaninsu da jami’an tsaro.

Sama da shekaru 15 ne mayaka masu ikirarin jihadi dake da alaka da Al-Qaeda ke kaddamar da hare-hare kan gwamnati da ke samun goyon bayan kasashen duniya da kuma otal-otal, wadanda suka saba karbar manyan jami’an Somaliya da na kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.