Isa ga babban shafi

Somalia: An kawo karshen mamayar da Al-shebab suka yi wa wani Otel a Mogadishu

Bayan kwashe sa'o'i da dama, jami'an tsaron Somalia sun yi nasarar kawo karshen kawanyan da mayakan al-Shebab suka yi wa wani otel a Mogadishu babban birnin kasar, kamar yadda kafafen yada labarai biyu na gwamnatin kasar suka sanar da sanyin safiyar yau Asabar, ba tare sun yi karin bayani kan harin na jiya jumma’a ko adadin wadanda lamarin ya shafa ba.

Wani sojan Somaliya tsaye a tagar otal din Pearl Beach da Al-shebaab suka kai wa hari a Mogadishu, 10/06/23
Wani sojan Somaliya tsaye a tagar otal din Pearl Beach da Al-shebaab suka kai wa hari a Mogadishu, 10/06/23 AP - Farah Abdi Warsameh
Talla

Tashar talabijin ta SNTV ta ce, jami’an tsaro sun kashe 'yan ta'addar da suka killace otal din Pearl Beach"  dake gabar tekun Liido a kudu da Mogadishu babban birnin kasar.

Yayin da kamfanin dillancin Labaran SONNA ya sanar da ceto fararen hula da dama a otel din da aka kaiwa harin.

Kazalika majiyoyin tsaro da na leken asiri sun tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa an kawo karshen wannan kawanya.

Kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin, inda ta ce ta kai hari a wani wurin da hukumomi ke yawan zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.